速報APP / 教育 / Jinin Haila Da Hukuncinsa

Jinin Haila Da Hukuncinsa

價格:免費

更新日期:2019-07-21

檔案大小:3.6M

目前版本:1.2

版本需求:Android 4.1 以上版本

官方網站:mailto:abdulmalikyahyabashir8@gmail.com

Jinin Haila Da Hukuncinsa(圖1)-速報App

Ma’anar (Haila) a shari’a

Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba.

Siffar Yadda Jinin Haila Yake

Jinin Haila Da Hukuncinsa(圖2)-速報App

Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo.

Shekarun Fara Jinin Haila

Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce.

Jinin Haila Da Hukuncinsa(圖3)-速報App

Tsawon Lokacin Haila

Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu.

Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa – “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka” [Abu Dawud ne ya rawaito shi]

Jinin Haila Da Hukuncinsa(圖4)-速報App

Mas'aloli

A qa'ida mai ciki ba ta yin haila, idan kuwa ta ga jini kafin haihuwarta da kwanaki kaxan, tare naquda, to wannan jinin biqi ne.

Jinin Haila Da Hukuncinsa(圖5)-速報App